Koyi Lissafi da kanka/ki cikin sauki a Hausamath.
Ire-iren Lissafi da misalansu cikin harshen Hausa.
Auna fahimtarka/ki ta hanyar daukar jarrabawa a Hausamath.
Hausamath Manhaja ce da aka kirkiro domin saukaka koyo da koyarwa na lissafi a cikin harshen Hausa. Kasancewar karatun lissafi ya dade yana bada wahala ga dalibai, sakamakon rashin hanyoyi na zamani da zasu taimaka wajen koyonsa, wannan ya kara bayar da kaimi wajen tabbatuwar wannan shafi na Hausamath.
Taimaka mana wajen tura zabi da kake ganin ya dace da wannan Shafi na Hausamath. Zamuyi amfani da bayanan da muka samu wajen kara inganta aikinmu
Wadannan kadanne daka cikin irin bangori na lissafi da muka bayar da damar koyonsu a wannan shafin na Hausamath.